Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta samu nasara wajen yaƙi da satar motoci, inda ta kama mutane uku da ake zargi tare da kwato manyan motocin da aka sata guda biyu.
A cikin bayanin da rundunar ta fitar, an ce wata motar Toyota Corolla da aka sace daga wani wajen sayar da motoci a kan titin Katsina a ranar 4 ga watan Agusta, 2025, an gano ta a Kabuga, a ranar 30 ga watan Agusta. An kuma kama wanda ake zargi, Zubairu Usman, bayan bincike mai zurfi.
Haka zalika, a wani lamari daban, an sace wata Toyota Hilux daga wani gida a titin Hadejia a ranar 25 ga watan Agusta. Motar ta kasance a hannun wani dillalin mota, Yallah Kadara, wanda ya amsa cewa ya sayi motar daga babban wanda ake zargi, Alamin Tasiu. Hakanan an kama abokan aikinsa biyu, Jacob Augustine da Sa’adu Bello, bisa rawar da suka taka wajen satar da kuma sayar da motar.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, PhD, ya yaba da ƙwazon jami’an rundunar wajen gudanar da bincike da kame waɗanda ake zargi. Ya kuma bukaci al’umma da su ci gaba da kasancewa masu faɗakarwa, tare da sanar da hukumomi duk wani abin da suka ga ba daidai ba a unguwanninsu, ta hanyar zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko kuma kiran layukan gaggawa.