Sabon rahoton rashin aikin yi a tsakanin matasa ya bayyana cewa rashin aikin yi a tsakanin matasan Najeriya ya haura zuwa kashi 53%, wanda aka bayyana a matsayin babbar barazana ga makomar ƙasar.
Rahoton, wanda Plan International Nigeria tare da Action Aid Nigeria suka fitar a Abuja yayin bikin ranar matasa ta duniya, ya nuna cewa miliyoyin matasa na fuskantar ƙarancin damar aiki, rashin tsaro, da kuma gazawar tsarin mulki, abin da ke tilasta su yin hijira ba bisa ka’ida ba, damfara ta yanar gizo, da sauran dabarun yin rayuwa masu haɗari.
Jonathan Abakpa, wanda ya gabatar da rahoton, ya ce:
“Wannan ba wai ƙididdiga ba ce kawai, alama ce ta burin da aka rushe da baiwar da aka yi asara. Idan ba a ɗauki matakan gaggawa ba, Najeriya na cikin haɗarin rasa amfanar matasan ta.
Rahoton ya bayyana cewa fiye da dalibai miliyan 1.7 ke kammala jami’a a kowace shekara, amma yawancinsu ba sa samun aikin yi. Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta nuna cewa rashin aikin yi ya ƙaru da kashi 5.3 cikin dari a farkon shekarar 2024, tare da ɗan ƙaramin sauƙi a ƙarshen shekarar.
Baya ga haka, rahoton ya nuna cewa fiye da mutane miliyan 82.9 ne ke rayuwa a talauci, tare da matsalolin da suka haɗa da cin hanci, rashin ingantaccen tsari, da kuma ƙarancin fasahar zamani.
Sai dai duk da wannan matsin lamba, rahoton ya yabawa jajircewar matasan Najeriya, musamman a fannin fasaha da masana’antar kirkire-kirkire. Ya yi kira da a ƙara samar da ayyuka, horaswa ta sana’o’in zamani, tallafin jama’a ga marasa galihu, da kuma tabbatar da cewa ilimin asali ya zama haƙƙin da kundin tsarin mulki ya tanada.
Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Harkokin Matasan Najeriya, Ayodeji Alao-Akala, ya tabbatar da cewa majalisar za ta ci gaba da tallafawa manufofin da suka shafi matasa.