Gwamnatin Kano ta sanar da ranar komawa makarantu

0
25

Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana ranar 7 da 8 ga Satumba, 2025 a matsayin ranar da za a koma makarantu na firamare da na gaba da firamare a jihar, domin fara sabon zangon karatu na shekarar 2025/2026.

Wannan sanarwa ta fito ne daga Daraktan Wayar da Kan Jama’a na Ma’aikatar Ilimi, Malam Balarabe Abdullahi Kiru, a cikin wata takarda da aka fitar ranar Laraba.

A cewar sanarwar, makarantun kwana za su bude ranar Lahadi, 7 ga Satumba, yayin da makarantun jeka ka dawo za su koma aiki a ranar Litinin, 8 ga Satumba.

Iyaye da masu kula da yara sun samu gargadi da su tabbatar da cewa ’ya’yansu sun koma makaranta akan lokaci, domin gwamnati ta bayyana cewa duk wani ɗalibi da ya saba da jadawalin dawo wa zai fuskanci hukunci.

Kwamishinan Ilimi na jihar, Dr. Ali Haruna Makoda, ya yi fatan alheri ga malamai da ɗalibai a yayin da suke shirin sabon zangon karatu, tare da tabbatar da cewa ma’aikatar za ta ci gaba da sa ido akai-akai a makarantu domin tabbatar da tsari da inganci a harkar koyarwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here