Dangote ya yiwa direbobin manyan motocin gargaɗi mai zafi

0
41

Kamfanin Dangote, ya sake yin gargadi ga direbobin manyan motocin sa, kan amfani da tambarin kamfanin a jikin motocinsu ba tare da izini ba, yana mai cewa hakan na jawo wa kamfanin abin kunya da kuma bata masa suna.

Kamfanin ya bayyana cewa duk da gargadin da aka sha yi a baya, wasu direbobi da ba su da alaka da Dangote na ci gaba da amfani da tambarinsa domin biyan bukatunsu na kansu, inda wasu daga cikin motocin suka sha shiga cikin hadurra da ake dangantawa da Dangote ba bisa ka’ida ba.

Dangote ya ce zai kara kaimi wajen sa ido tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro domin kamo masu laifi tare da daukar matakin doka a kansu.

> “Mun sha yin gargadi cewa a daina amfani da tambarinmu a motocin da ba mallakin kamfanin mu bane. Daga yanzu, za mu kara tsaurara bincike tare da daukar matakin shari’a kan duk wanda aka samu yana yin amfani da tambarinmu ba tare da izini ba,” in ji sanarwar da kamfanin ya fitar.

Haka kuma kamfanin ya nuna damuwa kan yaduwar labaran karya da ake dorawa a kansa, musamman danganta shi da hadurra a tituna ba tare da hujja ba. Ya bukaci al’umma da kafafen yada labarai su rika tabbatar da sahihancin labarai kafin wallafawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here