Ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Kiru/Bebeji a Kano, Abdulmumin Jibrin, ya bayyana cewa ba abin mamaki bane idan ya bar jam’iyyar NNPP.
Jibrin, wanda ya kasance na kusa da jagoran jam’iyyar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce ya isa ya yanke wa kansa shawara kan abin da ya dace da shi a siyasance. Ya kara da cewa ya shiga tafiyar Kwankwasiyya a matsayin mai kudi, kuma ya ba da gudummawa da dama ga tafiyar, duk da cewa ita ma ta taimaka masa wajen komawa majalisar a 2023.
A cewarsa, jam’iyya kanta ta ce a bude take don tattaunawa da sauran jam’iyyu, don haka ba dole ne na bi kowane mataki ba. Zan iya ci gaba da zama a NNPP, na koma APC, PDP, ADC ko PRP. Kowane lokaci na yanke shawara, zan bayyana wa jama’a.”
Duk da yiwuwar ficewarsa, Jibrin ya ce zai ci gaba da girmama Kwankwaso, kamar yadda bai taba zagin tsohon gwamna Abdullahi Ganduje ba tun lokacin da suka rabu.
Jibrin, wanda ke cikin ƴan adawa a yanzu, ana ganin yana da kusanci da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kasancewarsa daraktan yaƙin neman zaɓen sa a 2023 kafin ya koma NNPP.
A kwanakin baya, an ga ya kai ziyara sau biyu fadar shugaban kasa inda ya tattauna da Tinubu kan batutuwan da ya kira na ci gaban kasa.
Masu sharhi na siyasa suna ganin hakan na iya zama wani shiri na komawar Kofa, APC tare da Kwankwaso.