Ƙungiyoyin farar hula, masu ruwa da tsaki a harkar mai, da jam’iyyun adawa sun yi kakkausar suka kan shirin gwamnatin tarayya na aiwatar da harajin kashi 5% a kan man fetur da dizal daga ranar 1 ga Janairu, 2026.
Ƙungiyar masu gidajen mai (PETROAN) ta gargadi cewa idan aka tilasta wannan doka, wasu daga cikin ’ya’yanta na iya rufe sana’o’in su.
Ƙungiyar Joint Action Front (JAF) ta bayyana cewa za ta shirya taron nuna adawa tare da wayar da kan al’umma don hana aiwatar da dokar, tana mai kiran harajin “tursasawa ga talakawa”.
Jam’iyyar ADC da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023, Peter Obi, sun bayyana cewa wannan haraji zai ƙara tsananta talauci da tashin farashin kayayyaki a ƙasar. Obi ya ce bai dace a ɗora wa talakawa sabon nauyi ba a lokacin da gwamnati ke ikirarin samun ƙarin kuɗaɗen shiga.
Masana irin su Juliet Alohan-Ukanwosu na Extractive360 da Tijan Bolton na Policy Alert sun yi gargadi cewa ƙarin harajin zai haifar da tashin farashin sufuri, kayayyakin masarufi, da kuma ƙara jefa gidaje masu ƙaramin ƙarfin tattali cikin wahala.
Sai dai gwamnatin tarayya ta ce an kafa wannan doka ce domin ƙara samun kuɗaɗen shiga ba tare da dogaro da man fetur kawai ba, da kuma tabbatar da ɗorewar tattalin arziƙi.