Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bar Abuja a yau, Alhamis 4 ga Satumba, domin fara hutun shekara ta 2025.
Sanarwar da fadar shugaban ƙasa ta fitar ta bayyana cewa shugaban zai yi hutu na kwanaki goma a Turai, inda zai shafe lokacin sa a tsakanin ƙasashen Faransa da Birtaniya kafin dawo wa Najeriya.
Mai Bawa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin Bayani da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau.