Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa Najeriya na kan turbar cimma burin samun kuɗaɗen shiga wanda ba daga fannin man fetur ba, bisa rahotannin baya-bayan nan da suka nuna gagarumar ƙaruwa a tara kuɗaɗe daga fannoni daban-daban.
Wani jawabi da mai bawa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Laraba ya ce ƙaruwar da aka samu a fannin tara kuɗaɗen ya biyo bayan sauye-sauyen tsarin kuɗi, Ingantaccen karɓar haraji da kuma amfani da fasahar zamani wajen tara haraji da kudaden shiga.
A cewar rahoton, tsakanin watan Janairu zuwa Agusta na shekarar 2025, an samu kuɗaɗen shiga har Naira tiriliyan 20.59 daga fannoni da ba na man fetur ba, wanda ya haura da kashi 40.5% idan aka kwatanta da Naira tiriliyan 14.6 da aka samu a irin wannan lokaci a shekarar 2024.
“Wannan shi ne mafi ƙarfi a tarihin kuɗaɗen shiga na Najeriya a ‘yan shekarun nan. A karon farko cikin dogon lokaci, ba man fetur ne ya fi rinjaye wajen samar da kuɗin shiga ba,” in ji Onanuga.
Fadar Shugaban Ƙasa ta danganta wannan nasara da sauye-sauye na tsarin tattalin arziki, ciki har da ƙarfafa aiwatar da dokoki, amfani da na’urorin zamani a Hukumar Kwastam, da kuma biyan haraji ta yanar gizo.
Daga cikin jimillar kuɗaɗen da aka samu, kuɗaɗen da ba daga man fetur ba sun kai Naira tiriliyan 15.69, wato kashi uku bisa huɗu na dukkanin tarin kuɗin shiga. Hukumar Kwastam kaɗai ta tara Naira tiriliyan 3.68 a rabin farkon shekarar 2025, abin da ya fi burin da aka sanya da Naira biliyan 390.
Onanuga ya ce matakin gaba shi ne tabbatar da cewa waɗannan nasarori sun tabbata a rayuwar ‘yan ƙasa ta hanyar samar da ingantattun makarantu, asibitoci, hanyoyi da kuma samar da ayyukan yi.