Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa muhimman tsare-tsaren da gwamnatinsa ta ɗauka sun haifar da sakamako mai kyau, tare da janyo hankalin masu zuba jari daga ƙasashen duniya.
Tinubu ya faɗi haka ne a fadarsa da ke Abuja yayin da yake karɓar baƙuncin Oba Ghandi Afolabi Oladunni Olaoye, Orumogege III na Ogbomoso, tare da tawagarsa.
Shugaban ya ce matsalolin rashawa, fasa kauri da yaudara sun dade suna hana Najeriya samun kuɗaɗen shiga da za a yi amfani da su wajen samar da ci gaba.
“Tattalin arziƙin mu ya fuskanci barazana, wajibi ne mu ɗauki matakai ƙwarara don gyara shi. Amma tare da addu’o’inku da haƙuri da juriyarku, ina farin cikin shaida muku cewa a yanzu tattalin arziƙi ya dai-daita,” in ji Tinubu.