Wani mutum mai suna Yusif Musa, ya gurfanar da shugaban kwamitin unguwar Yankusa, Abdulaziz Isa, a gaban kotun shari’ar Musulunci da ke Danbare, karkashin jagorancin Alkali Munzali Idris Gwadabe.
Yusif, ya bayyana wa kotu cewa yana soyayya da wata bazawara mai suna Amira Abubakar, har ma sun kai ga yin gwajin jini domin shirya aure. Sai dai, a cewarsa, shugaban kwamitin unguwar su bazawarar tasa tare da wasu ‘yan uwan sa sun tsoma baki, suna hana neman shi hulɗa da Amira, inda suka kai ga korar sa daga kofar gidan masoyiyar tasa.
Mai karar ya kara da cewa, kimanin makonni biyu da suka wuce, Abdulaziz ya hana shi zuwa gidan bazawarar duk da cewa ya kashe kusan ₦70,000 wajen zirga-zirgar abin hawa da kuma siya wa ɗan Amira kayan ciye-ciye.
Bisa wannan dalili ne Yusif ya nemi kotu ta sa a biya shi kudin da ya kashe, yana mai cewa ya kai korafinsa har ofishin kwamitin unguwar.
Alkalin kotun, Munzali Idris Gwadabe, ya umurci a mika lamarin ga rundunar ‘yan sanda domin fadada bincike.