Karyewar farashin ɗanyen man fetur na barazana ga kasafin Kuɗin Najeriya

0
6

Farashin man fetur ya sauka a ranar Alhamis kafin taron kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta duniya, OPEC da kawayenta da za a gudanar nan da kwanaki uku.

Farashin ganga ɗaya ta ɗanyen man ya ragu da kashi 1.11 cikin 100 zuwa dala $66.85, yayin da man Amurka ya sauka da kashi 1.20 cikin 100 zuwa dala $63.20 kowace ganga.

Rahotanni sun nuna cewa a ranar Lahadi, kasashe guda takwas da suka hada da Saudiyya, Rasha, Iraki, Hadaddiyar Daular Larabawa, Kuwait, Kazakhstan, Aljeriya da Oman za su tattauna kan yiwuwar karin samar da man fetur a watan Oktoba.

A baya dai, a ranar 5 ga Disamba 2024, OPEC ta sanar da tsawaita gyare-gyaren samar da man fetur har zuwa karshen Maris 2025, inda aka tsara rage ganga miliyan 2.2 a kullum a hankali har zuwa karshen Satumba 2026 don daidaita kasuwar man.

Sai dai daga ranar 1 ga Afrilu 2025, ƙasashen suka amince da kara samar da man fetur, wanda ya ci gaba a watanni masu zuwa da karin dubban ganguna a kowanne wata.

Masana sun yi gargadin cewa faduwar farashin man fetur kasa da $75 kowace ganga, wanda aka yi amfani da shi a matsayin tsari a kasafin kudin Najeriya na 2025 na iya zama barazana ga aiwatar da kasafin kudin kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here