Hukumar yaƙi da cin hanci, ta gayyaci shugaban ƙaramar hukumar Dala, da shugaban Kwalejin Legal

0
21

Hukumar karɓar koke-koke da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta gayyaci shugaban ƙaramar hukumar Dala, da shugaban Kwalejin nazarin addinin musulunci da harkokin shari’a ta Kano, wadda akafi sani da Legal.

Shugaban hukumar Sa’idu Yahaya, ne ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai, bayan wata ziyarar da hukumar ta kai wasu daga cikin ma’aikatun dake ƙarƙashin kulawar gwamnatin jihar don ganin yadda suke aiwatar da ayyukan su.

A lokacin wannan ziyara mun ziyarci gurare uku da suka ƙunshi asibitin kwararru na Murtala, Sakatariyar ƙaramar hukumar Dala, da Kwalejin Legal, inji Sa’idu.

Yace basu ji dadin yadda suka tarar da sakatariyar ƙaramar hukumar Dala ba, sakamakon ƙaramar hukumar tana da daraktoci 8, amma daya ne kawai yake a bakin aiki, sai Kwalejin Legal, da ba’a samu shugaban ta a bakin aiki ba, sai maga takardan Kwalejin shima baya nan, sannan sakataren harkokin koyarwa na Kwalejin shima baya bakin aiki.

Shugaban hukumar yace, shi kuwa asibitin kwararru na Murtala, basu aikata laifin komai ba, saboda an samu kowa a bakin aiki, yadda ya kamata, don haka ne ma ya yabawa hukumar gudanarwar asibitin.

Daily News 24 Hausa, ta rawaito cewa, Sa’idu Yahaya, yace waɗanda aka gayyata zasu zo domin bayyana dalilin rashin zuwan wasu daga cikin ma’aikata aiki, da kuma daukar matakan gyara don hana hakan sake faruwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here