Har yanzu Kwankwaso zai iya komawa jam’iyyar APC – Jibrin

0
15

Abdulmumin Jibrin, dan majalisar tarayya mai wakiltar Kiru da Bebeji, kuma babban jigo a jam’iyyar NNPP, ya bayyana cewa tsohon gwamnan Kano kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, na iya sake komawa jam’iyyar APC.

Jibrin ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, lokacin ake zantawa dashi a kafar telebijin ta Channels, inda ya ce Kwankwaso bai rufe kofar tattaunawa da jam’iyyar mai mulki ba, musamman yiwuwar hada kai da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

A cewar Jibrin, Kwankwaso ko yaushe yana bude kofar tattaunawa a fagen siyasa, don haka haɗin gwiwa da APC na nan a matsayin wata dama mai yiwuwa.

Sai dai lokacin da aka tambayi Jibrin game da shirin kansa na siyasa, ya ce yana daukar matsaya ne bisa ga ra’ayinsa, ba tare da sai ya nemi amincewar Kwankwaso ba, koda yake yana cikin tafiyar Kwankwasiyya.

A baya-bayan nan dai, Kwankwaso ya musanta jita-jitar cewa yana shirin barin NNPP, inda ya jaddada cewa duk wani mataki kan zaben 2027 za a yanke shi ne tare da sauran jiga-jigan jam’iyyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here