Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano ta bayyana cewa duk mai niyyar zuwa aikin Hajjin 2026 dole ne ya ajiye kuɗi naira miliyan 8 da dubu 500 (₦8.5m) a matsayin kuɗin rajista.
Daraktan Hukumar, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ne ya bayyana haka yayin wani taro da ya gudanar tare da shugabanni da jami’an hukumar a matakin ƙananan hukumomi.
A cewar sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Malam Sulaiman Dederi, ya fitar a ranar Laraba, an bayyana cewa wannan kuɗi an tsara shi ne bisa tsarin da Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta fitar, kuma za a karɓa ta hanyar bank, da za a miƙa ta ofisoshin ƙananan hukumomi na hukumar alhazai.
Hukumar ta kuma tabbatar da cewa Kano ta samu kujeru 5,684 daga NAHCON domin aikin Hajjin shekarar 2026.
Sanarwar ta ƙara da cewa za a fara karɓar kuɗin ajiya nan take, kuma za a rufe karɓar a ranar 5 ga Oktoba, 2025, lokacin da za a fitar da kuɗin hajjin ƙarshe.
Alhaji Danbappa ya shawarci masu niyyar zuwa aikin Hajji da su gaggauta biyan kuɗin ajiya domin kaucewa rasa damar zuwa, tare da tunatar da su cewa dole ne a samu fasfo na ƙasa da ƙasa da kuma hotuna guda takwas na maniyyaci kafin a kammala rijista.