Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana damuwarta kan abin da ta kira maimaita korar ‘yan Arewa daga Babban Birnin Tarayya Abuja zuwa Kano da wasu jihohin Arewacin Najeriya.
Kwamishinar Mata, Yara da Masu Bukata ta Musamman, Hajiya Amina Sani-Abdullahi, ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis a Kano.
Ta ce cikin makonni hudu da suka gabata, an tilasta wa ‘yan Najeriya da dama ciki har da mazauna Kano, Jigawa, Katsina da Kaduna barin Abuja tare da mayar da su Kano.
Kwamishinar ta jaddada cewa wannan mataki ya saba wa ‘yancin kowane ɗan kasa na zama da neman arziki a duk sassan Najeriya muddin bai karya zaman lafiya ba.
“Abuja ba mallakar wata jiha ko yanki guda ɗaya ba ce. Wurin hadin gwiwa ne na dukkan ‘yan Najeriya, kuma kowa na da hakkin zama da neman abin yi a can,” in ji ta.
Hajiya Amina ta ce maimakon korar mutane, abun da ya dace shi ne a kirkiro shirye-shiryen tallafa musu, samar da horo, da kuma hanyoyin samun na kansu.
Ta kuma yi nuni da cewa rahotanni daga wasu daga cikin wadanda aka koro sun nuna cewa an tsare su sama da kwanaki goma a yanayi mara kyau, tare da samun abinci sau ɗaya a rana.
Ta bayyana wannan danyen aiki a matsayin cin mutunci da kuma abin kunya ga tsarin dimokuraɗiyya.
Kwamishinar ta kara da cewa gwamnatin Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ba za ta lamunci cin mutuncin jama’ar ta ba.
“Muna kira ga hukumomin Abuja, su duba wannan tsari na kora, su kuma dauki matakai na doka da kuma tausayi wajen magance irin wannan batu nan gaba,” in ji ta.