An ci amana ta a zaɓen shekarar 2015–Goodluck

0
33

Tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ya ce ya fuskanci cin amana sosai a lokacin da yake neman zarcewa kan kujerar shugabancin ƙasa a zaben 2015.

Jonathan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin bikin cika shekaru 70 na tsohon shugaban ma’aikatansa, Chief Mike Aiyegbeni Oghiadomhe, a Benin, babban birnin jihar Edo.

Ya ce siyasar Najeriya, cike take da cin amana, inda yawancin ‘yan siyasa ke da wuya su tsaya kan maganar da suka faɗa jiya su sake nanatawa yau.

“Na ga abubuwa da dama a lokacin zaɓen 2015. Mutane za su gaya maka abu ɗaya da safe, amma kafin rana ta kare sai su canja magana,” in ji shi.

Sai dai Jonathan ya bayyana cewa Oghiadomhe ɗaya ne daga cikin abokansa na gaskiya da yake iya tsayawa a bayansa a kowane hali. “Shi mutum ne da zaka iya ɗaukar maganarsa da muhimmanci. Yana daga cikin kaɗan waɗanda ba za su yi watsi da kai ba.”

Oghiadomhe ya rike matsayin shugaban ma’aikata a fadar shugaban ƙasa tsakanin 2010 zuwa 2014.

Taron ya samu halartar manyan baki da suka haɗa da Sanata Adams Oshiomhole, tsohon gwamnan Edo Lucky Igbinedion, tsohon gwamnan Gombe Ibrahim Dankwambo, Chief Tom Ikimi, lauya Mike Ozekhome (SAN), da kuma shugabar UBTH, Farfesa Izia Ize-Iyamu, da sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here