’Yan daba sun tarwatsa taron zaman lafiya a Katsina

0
8

Wasu matasa da ake zargin ’yan daba ne sun tarwatsa wani taro da dattawan Katsina suka shirya domin tattauna hanyoyin magance matsalar tsaro a jihar, a ranar Talata.

Taron, wanda ƙungiyar Katsina Security Community Initiative ta shirya, ya tattara masana, tsofaffin jami’an tsaro, malamai da shugabannin al’umma domin lalubo mafita kan hare-haren ’yan bindiga da ke addabar jihar.

Sai dai jim kaɗan bayan fara taron, rikici ya ɓarke lokacin da Dr. Bashir Kurfi, wanda ya shirya taron, ya fara jawabi inda ya zargi cewa yawancin kananan hukumomin jihar sun zama kufai sakamakon hare-haren ’yan bindiga.

Wani mutum ya katse jawabin nasa yana zargin shi da yin adawa da gwamnati, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce tsakanin magoya bayan gwamnati da masu goyon bayan taron.

Bayan haka ne aka fara jifa da kujeru, tare da kai wa manema labarai hari.

 Rahotanni sun ce an girke ’yan daba a wurin taron, inda wasu daga cikinsu suka rika nuna wukake suna yi wa mahalarta taron barazana.

Duk da tarwatsuwar taron, Dr. Kurfi ya dage cewa ba za su ja da baya ba wajen ci gaba da fafutukar samar da zaman lafiya a Katsina. Ya kuma zargi gwamnatin jihar da hannu a kai harin yana mai cewa ’yan dabar na da alaka da gwamnatin Katsina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here