Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya ce kafa ’yan sandan jihohi ya zama wajibi domin ƙara ƙarfafa tsaro a ƙasar nan.
Tinubu ya bayyana haka ne a fadar sa, yayin da ya karɓi wata tawagar manyan mutanen Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dikko Radda.
Shugaban ya ce gwamnatin tarayya ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yaki da matsalar tsaro, musamman a Katsina da ta fuskanci ƙaruwa wajen hare-haren ‘yan bindiga.
Kalubalen tsaro da muke fuskanta abu ne da za mu iya shawo kansa da tsari da jajircewa. Na ba da umarni a ƙara sayen kayan aikin zamani, kuma ina nazarin batun kafa ’yan sandan jihohi a matsayin mafita mai dorewa, inji shi.
Ya ƙara da cewa dole ne a kare rayukan ‘yan ƙasa, wuraren ibada, kasuwanci da kuma wuraren nishaɗi daga barazanar ‘yan ta’adda.
A nasa jawabin, Gwamna Radda ya godewa Tinubu kan yadda yake amsa bukatun Jihar Katsina, yayin da sauran shugabanni irin su tsohon Gwamna Aminu Masari da Wazirin Katsina, Ibrahim Ida, suka yaba da irin jarumtaka da tallafin da shugaban ƙasar ke baiwa jihar.