Likita ya rasu sakamakon gajiyar aikin awanni 72 babu hutu

0
20

Wani likita mai neman ƙwarewa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Rivers (RSUTH), Oluwafemi Rotifa, ya rasu bayan da ya yi aikin awanni 72 ba tare da hutu ba.

Rahotanni sun nuna cewa Rotifa ya fadi a dakin hutun ma’aikata a ranar Litinin, daga bisani aka kai shi dakin kulawa ta musamman (ICU), amma duk da ƙoƙarin da aka yi, ya rasu.

Shugaban ƙungiyar likitoci masu neman kwarewa ta ƙasa (NARD), Tope Osundara, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana damuwarsa kan yadda yawan aiki ke haddasa gajiya mai tsanani ga likitoci a ƙasar nan.

“Likitan yana kan aiki a dakin bayar da kulawar gaggawa, inda nauyin aiki ya yi tsanani sosai. Bayan ya kammala duba wani mara lafiya, ya je dakin hutu, amma daga baya aka same shi a ƙasa,” in ji shi.

Osundara ya ƙara da cewa wasu likitoci a Najeriya na shafe har wata ɗaya suna shiga aiki ba tare da isasshen hutu ba, abin da ya ce ya saba ƙa’ida.

Ya kuma bayyana cewa Rotifa yana fama da cutar zazzabin cizon sauro (malaria), amma saboda ƙarancin ma’aikata ya ci gaba da aiki duk da halin rashin lafiyar da yake ciki.

Ƙungiyar likitocin ta bukaci gwamnati da ta ɗauki mataki wajen:

ƙara yawan ma’aikatan lafiya,

inganta walwalar likitoci,

da kuma tsara jadawalin aiki mai sauƙi domin kare lafiyar ma’aikata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here