Gwamnatin Kano ta ja kunnen ACF akan kafa majalisar dattawan jihar

0
5

Gwamnatin jihar Kano ta gargadi ƙungiyar tuntuɓa ta arewa  (ACF) kan shirin ta na kafa sabuwar majalisar dattawan Kano.

A cewar gwamnatin, tun a watan Janairu 2024 ne gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa Majalisar Dattawan Jihar Kano (KEAC), wadda aka tsara domin bayar da shawarwari kan ci gaban al’umma.

Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na jihar, Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba.

Ya ce tun bayan ƙaddamar da shirin kafa wannan majalisa, ana ci gaba da shirye-shiryen da suka dace domin tabbatar da ingantaccen tsarin da zai bai wa majalisar damar fara aiki yadda ya kamata.

Gwamnatin ta bayyana cewa wannan majalisa ba ta da alaƙa da kowace jam’iyya ko siyasa, sai dai dandalin bayar da shawarwari ta hanyar hikima da gogewa.

An bayyana cewa majalisar za ta ƙunshi fitattun mutane daga Kano, ciki har da tsofaffin shugabanni, alƙalan kotuna, malamai, sarakuna, ‘yan kasuwa da kuma shugabannin tsaro.

Haka kuma, gwamnatin ta bukaci dukkan ƙungiyoyi da al’ummomi su haɗa kai da tsarin da aka kafa maimakon ƙirƙirar wani sabon tsari.

A cewar sanarwar, hakan zai taimaka wajen ƙarfafa ayyukan majalisar tare da tabbatar da cimma manufar kawo ci gaba da haɗin kai ga jama’ar Kano.

An ƙara da cewa, nan ba da jimawa ba za a kammala dukkan shirye-shirye kafin gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da majalisar a hukumance.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here