Gwamnati tarayya ta cire tallafin gas ɗin ababen hawa

0
33

An samu tashin farashin gas ɗin ababen hawa (CNG) wanda ya tashi daga Naira 230 zuwa Naira 450 kan kowace mita daya, lamarin da ya janyo dogayen layuka a wuraren zuba gas ɗin.

Bincike ya gano cewa gwamnatin tarayya ta duba farashin a kwanan nan tare da rage tallafin da take bayar wa a kan sa.

 Duk da haka, direbobin motocin haya da masu motocin gida na amfani gida da wani rangwamen farashi inda suke biyan Naira 380, yayin da manyan motoci masu ɗaukar kaya ke biyan cikakken farashi na Naira 450.

Wani jami’i na Shirin CNG na Fadar Shugaban Ƙasa (PCNGI) ya tabbatar da wannan canji, koda yake bai so a bayyana sunansa ba. Ya ce an yi hakan ne domin rage tashin kuɗin sufuri ga fasinjoji.

Farashin yanzu yana banbanta da nau’in mota. Motocin haya da na fasinja suna da rangwamen farashi, amma manyan motoci masu ɗaukar kaya suna biyan cikakken farashin gas ɗin,” in ji shi.

Jami’in ya ƙara da cewa babban burin shirin PCNGI shi ne samar da karin tashoshin cika gas a ƙasar domin rage dogayen layukan da ake fuskanta a halin yanzu.

 “Muna so mu gina karin tashoshin CNG a sassan ƙasa don masu motocin da aka mayar su sami isasshen gas. Idan tashoshi ba su da yawa, masu mota sai su koma amfani da fetur,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here