Gwamnati ta ayyana Juma’a a matsayin hutu don bikin Maulidi

0
16

Gwamnatin tarayya ta ayyana Juma’a, 5 ga watan Satumba, a matsayin ranar hutu domin bikin Maulidin Annabi Muhammad (S.A.W).

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin cikin gida ta fitar a ranar Laraba, tare da sa hannun babbar sakatariyar ma’aikatar, Magdalene Ajani.

A duk shekara, miliyoyin Musulmi a Najeriya da sauran sassan duniya kan gudanar da bukukuwan Maulidi domin tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W).

Gwamnati ta kuma yi kira ga al’ummar ƙasar da su yi amfani da wannan lokaci wajen roƙon Allah ya kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali, musamman ganin yadda ake fama da matsalolin tsaro a ƙasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here