Civil Defence Sun Kama Masu Satar Kayan Wutar lantarki a Kano

0
3

Rundunar tsaron a’lumma ta farin kaya NSCDC reshen jihar Kano ta kama wasu matasa shida da ake zargi da lalata kayayyakin wutar lantarki a unguwannin Hayin Da’e da Hotoro da ke karamar hukumar Tarauni.

Mai magana da yawun hukumar, Ibrahim Abdullahi, ya bayyana cewa an kama su bayan samun sahihan bayanai daga jami’an bijilanti na yankin.

Waɗanda aka kama sune Muhammad Yusuf mai shekaru (18), Muhd Sani Adamu mai shekaru (19), Umar Musa mai shekaru (19), Ahmed Auwal, mai shekaru (20), Muhd Yusuf mai shekaru (28), da Usman Ali, mai shekaru (19).

 Rahotanni sun nuna cewa yawancin su mazauna yankin ne, kuma an kama su da wayar na’urar wutar lantarki da aka sace yayin wani samame da aka gudanar da tsakar dare.

Binciken farko ya tabbatar da cewa wadanda ake zargin suna da hannu a sata da lalata kayan wutar lantarki a yankunan Hayin Da’e, Farawa Kwanar Yashi da Hotoro Eastern Bypass.

Hukumar ta ce bincike na ci gaba kuma bayan kammalawa za a gurfanar da su a gaban kotu.

Kwamandan NSCDC a Kano, Shafi’u Abdulmumini, ya tabbatar wa jama’a cewa za su ƙara tsaurara tsaro da sa ido a dukkan sassan jihar don dakile irin wannan barna da sauran laifuka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here