An ƙona gidaje da gonaki masu yawa a jihar Filato

0
25

An ƙona gidaje da gonaki masu yawa a jihar Filato

Fiye da mutum 300 sun rasa matsugunnansu bayan hare-haren da aka kai a Karamar Hukumar Qua’an-Pan, a jihar Plateau, inda aka ƙona gidaje 30 tare da lalata gonaki da sauran dukiyoyi.

Hare-haren sun faru a ƙauyuka 10 da suka haɗa da Nteng, Doop, Zhep Morop, Gyeergu, Kelaghan, Loon, Kwakii da Gorom.

Shugaban karamar hukumar, Christopher Manship, ya yi kira ga shugabannin gargajiya, addinai da kungiyoyi su haɗa kai wajen ganin an kawo ƙarshen tashin hankalin dake faruwa a yanzu. Ya ce an tura jami’an tsaro yankin kuma gwamnati na yin aiki don dawo da zaman lafiya.

Kwamishinan al’adu da yawon bude ido na Plateau, Cornelius Doeyok, ya yaba da ƙoƙarin Manship na haɗa masu ruwa da tsaki domin shawo kan matsalar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here