Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin kudi na dala miliyan 32.5 ga Shirin Abinci na Duniya (WFP) domin taimaka wa ‘yan Najeriya da ke fama da matsalar yunwa, musamman wadanda rikice-rikice suka raba da gidajensu.
Wannan tallafi zai bai wa WFP damar kai agajin abinci mai gina jiki ga mutane sama da 764,000 a yankunan Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma, inda rikici ya fi yin barna.
Daga cikin masu amfana akwai mata masu juna biyu da masu shayarwa sama da 41,000, da kuma yara kusan 43,000, wadanda za su sami kariya daga matsalar rashin abinci mai gina jiki.
Shirin ya bayyana cewa wannan taimako daga gwamnatin Amurka zai taka muhimmiyar rawa wajen ceto rayuka, rage yunwa, da inganta lafiyar al’umma a yankunan da rikici ya dade yana addaba.