‘Yan sanda sun kama ƙwararrun masu safarar makamai a Katsina
Rundunar ’yan sandan jihar Katsina ta kama mutane biyu da ake zargi da safarar makamai, tare da kama manyan bindigogi da harsasai da suka shigo da su cikin jihar.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DCP Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana cewa an kama mutanen ne a kan hanyar Ingawa zuwa Karkarku da ke Katsina.
Masu safarar makaman da aka kama sun hada da Abdussalam Muhammed mai shekaru (25) da Aminu Mamman mai shekaru (23), dukkansu mazauna ƙaramar hukumar Safana. A cikin motar su kirar Golf mai lamba RSH-528 BV, ’yan sanda sun gano bindigar GPMG guda ɗaya, harsashin AK-47 guda 1,063, da harsashin PKT guda 232.
Bincike ya nuna cewa makaman na kan hanyarsu daga Hadejia, jihar Jigawa, zuwa Safana domin rabawa ga ’yan ta’adda.