Uwargidan Shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayyana cewa tana son bikin zagayowar ranar haihuwar ta, na 65 da za ta zo ranar Lahadi, 21 ga Satumba, 2025 ya kasance cikin natsuwa ba tare da shagulgula ba.
A maimakon kyaututtuka, katuna, ko furanni, ta roƙi masoya da abokan arziki su mayar da su zuwa gudummawar kuɗi domin ƙammala ginin babban ɗakin karatu na ƙasa da take son yi, abinda ta ce shi ne kyautar da tafi so a rayuwar ta.
Uwargidan ta ce wannan yunƙuri na daga cikin sha’awar ta ta tallafa wa ilimi, inda aka buɗe asusun musamman na “Oluremi at 65 Education Fund” a bankin Zenith don gudanar da aikin.