Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin a dawo da Salihu Abdullahi Dembos kan muƙamin sa, na matsayin shugaban tashar Talabijin ta ƙasa (NTA), wanda ya bar kujerar na ɗan lokaci sakamakon wasu canje-canjen shugabanci da akayi a hukumar gudanarwar tashar.
An naɗa Dembos a matsayin shugaban tashar tun a watan Oktoba 2023, kuma yanzu zai ci gaba da jagorantar hukumar har ya kammala wa’adin shekaru uku.
Haka kuma, Shugaban Ƙasar ya bada umarnin a dawo da Ayo Adewuyi, zuwa matsayin sa na Daraktan Labarai na NTA, domin ya ci gaba da wa’adinsa na shekaru uku wanda zai ƙare a shekarar 2027. An naɗa Adewuyi a wannan mukami a shekarar 2024.
Sabon umarnin Shugaban Ƙasar ya soke naɗe-naɗen da aka sanar a baya, kamar yadda Mai bawa Shugaban Ƙasa shawara kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a yau Talata.