Sarkin Zazzau ya koka kan karancin likitoci a Zariya

0
5

Mai martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu-Bamalli, ya bayyana damuwa kan ƙarancin likitoci a asibitocin da ke fadin masarautar sa.

Sarkin ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi tawagar kungiyar likitoci mata ta Najeriya (MWAN), kungiyar Clinton Health Access Initiative (CHAI), da wasu abokan hulɗa da suka kawo shirin bayar da agajin lafiya kyauta ga al’umma.

Ya ce duk da yawan jama’ar garin, akwai ‘yan kalilan daga cikin likitoci da ke bauta wa al’umma. Ya yi nuni musamman da Asibitin Janar na Gambo Sawaba, mafi girma a yankin, wanda ke fuskantar cunkoso na marasa lafiya kullum.

“Yawan jama’a da ke zuwa asibitin yana tilasta wasu daga cikin mutanenmu yin tafiyar kilomita 20 zuwa Asibitin Koyarwa na ABU, Shika, duk da cewa akwai asibitin Janar nan kusa da mu. Wannan abin takaici ne a ƙarni na 21,” in ji shi.

A nata jawabin, shugabar MWAN reshen Kaduna, Hajiya Aisha Mustapha, ta ce shirin na bayar da agaji wani bangare ne na taron kasa da suka shirya karo na 24.

Ta bayyana cewa an yi wa akalla mutane 1,000 hidima, ciki har da ƙananan tiyata, duba cutar mahaifa, kula da hakora, kula da ido, da kuma rabon tabarau ga masu fama da matsalar gani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here