Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta kama wasu kayayyakin da aka haramta amfani da su, a jihar Kano, inda ta gano kwalabe 8,000 na Akuskura da ake zargin na dauke da sinadarai masu illa, tare da ƙunshi 48 na tabar wiwi.
Kakakin hukumar a Kano, ASP Sadiq Muhammad Maigatari, ya tabbatar da cewa sun kama wani mutum mai shekara 37, Ali Muhammad, a kan titin Zaria zuwa Kano, a Gadar Tamburawa, bisa zargin aikata safarar ƙwayoyi.
Rahoton ya bayyana cewa an boye kayan cikin wata babbar da zata tafi Maiduguri, inda aka gano su tsakanin keke Napep dake cikin motar da kuma karkashin babbar motar.
Shugaban rundunar NDLEA a Kano, ACGN A.I. Ahmad, ya yabawa jami’an da suka kama kayan bisa wannan nasara tare da tabbatar da cewa ana ci gaba da bincike da gwaje-gwaje domin tabbatar da nau’in kayan.
NDLEA ta kuma shawarci jama’a da su rika kai rahoton duk wani abu ko motsi da ake zargin na da alaka da miyagun kwayoyi ga ofishinta mafi kusa ko kuma ga hukumomin tsaro.