Marafa: Zan Rage Wa Tinubu Kuri’a Miliyan Daya a 2027

0
26

Tsohon Sanatan Zamfara ta Tsakiya, Kabiru Marafa, ya ce zai tabbatar da cewa an rage wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kuri’a miliyan daya a zaben shugaban kasa na 2027.

Marafa, wanda ya fice daga jam’iyyar APC kwanan nan bayan zargin shugabancin Tinubu da salon “butulci ga wanda suka taimaka masa” ya bayyana haka a shirin Politics Today na Channels TV.

 “Ina tabbatar muku da abu guda, zan rage wa Shugaban kasa kuri’a miliyan daya daga wadanda ya samu a 2023. Na dauki wannan a matsayin kalubale, kuma da ikon Allah zan yi nasara,” in ji shi.

Ya ce duk da wasu na yi masa kallon mara tasiri a siyasa, zaben 2027 zai tabbatar da irin karfinsa. Marafa ya bayyana cewa a Zamfara, yawancin manyan ‘yan siyasa sun hade a waje guda domin kalubalantar APC.

Ya kuma zargi Tinubu da karya alkawuran da ya dauka, musamman na gyara tsarin rabon mukamai a jam’iyyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here