Ministan sufuri, Sa’idu Ahmed Alkali, ya tabbatar da cewa jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna da ya kauce hanya a makon da ya gabata, zai koma aiki cikin kwanaki goma nan gaba.
Idan za’a tuna a baya dai jirgin ya tuntsure a kusa da tashar Asham bayan ya baro Abuja zuwa Kaduna, yana ɗauke da mutum 618, ciki har da fasinjoji 583, ma’aikata 15, ma’aikacin jinya guda ɗaya da kuma masu tsaftace muhalli 11. A kalla fasinjoji bakwai ne suka samu raunuka a hatsarin.
A yayin wata ziyara da ya kai wajen da lamarin ya faru a jiya Litinin, Ministan ya yaba da yadda jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki suka tashi tsaye wajen kare rayukan fasinjoji da ma’aikata, tare da tabbatar da an kwashe su cikin lafiya.
“Lokacin da hatsarin ya faru, jirgin na tafiya da tarago guda bakwai. Zuwa yanzu an kwashe huɗu, kuma ana kan aiki don kwashe sauran. Muna da yakinin nan da kwana biyu za a gama, sannan cikin kwana goma idan Allah ya so jirgin zai koma aiki yadda aka saba,” in ji Alkali.