Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta bayyana cewa farashin cika tukunyar gas ɗin girki na 12.5kg ya ƙaru daga ₦14,261.57 a watan Yuli 2024 zuwa ₦20,609.48 a watan Yuli 2025, wanda hakan ya nuna ƙaruwa da kashi 44.5% cikin shekara ɗaya.
Duk da haka, hukumar ta ce an ɗan samu raguwa da kashi 1.91% daga watan Yuni zuwa Yuli 2025.
Rahoton ya nuna:
Jihohin da suka fi fuskantar tsadar sune, Adamawa (₦22,528.39), Rivers (₦22,512.49), Taraba (₦22,363.57)
Jihohin da suka fi araha sune, Yobe (₦19,030), Niger (₦19,154.99), Nasarawa (₦20,000.62)
Rahoton ya dogara ne da bayanai daga mutane fiye da 10,000 a fadin ƙasar nan.