Matatar man fetur ta Dangote dake Lagos, ta fara fitar da man fetur mai yawa zuwa kasashen waje, musamman bayan wasu masana’antun mai a Gulf suka rufe na’urorinsu don gyare-gyare.
Wata majiya daga cikin masana’antar ta shaida cewa a watan Agusta kadai, masana’antar ta fitar da man fetur (PMS), man dizal (AGO), da man jiragen sama (Jet A1) zuwa kasashen waje.
Rahotanni sun nuna cewa tun daga watan Yuni zuwa Yuli, Dangote ya riga ya kai kaya guda biyu na dogayen jiragen ruwa zuwa yankin gabas ta tsakiya. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar karancin man fetur a kasuwannin duniya, musamman saboda rufewar wasu manyan matatun mai a yankin.
Kamfanin Aramco na Saudi Arabia ya rufe wasu daga cikin matatun man sa biyu, tare da shirin rufe babbar matatar mai ta Satorp dake Jubail wadda ke tace ganga dubu 460 a rana na tsawon kwanaki 60 daga Nuwamba zuwa Disamba. Haka kuma, akwai shirin gyara a matatar man Riyadh a zangon karshe na shekarar nan.
Masana sun yi hasashen cewa wannan rufewa zata kara tsananta karancin man fetur a duniya, wanda hakan zai bai wa Dangote damar fitar da karin kaya zuwa kasashen ketare.