Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa komawar tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, cikin jam’iyyar PDP zai iya zama ƙarshen jam’iyyar gaba ɗaya.
Wike ya yi wannan magana ne a lokacin wata ganawa da manema labarai a Abuja, inda ya ce Obi ya taba kiran PDP a matsayin jam’iyyar da ta lalace, don haka bai dace a buɗe masa ƙofa ba domin ya sake yin takara a cikin ta.
Ya kara da cewa akwai mutane da dama da suka jajirce wajen tsare jam’iyyar tun bayan zaben 2023, don haka bai dace a bawa Obi tikitin takarar shugabancin kasa ba.
“Idan ana son rusa jam’iyyar PDP, to a dawo da Obi,” in ji Wike.
Obi ya bar PDP kwanaki kafin zaɓen fidda gwani na 2023, inda ya koma Labour Party, wadda ya tsaya a cikin ta a matsayin ɗan takara na shugaban ƙasa.
A wancan zaɓe, ya zo na uku da ƙuri’u 6,101,533, bayan Atiku Abubakar na PDP da ya samu 6,984,520, da kuma Bola Tinubu na APC wanda ya yi nasara da ƙuri’u 8,794,726.