Shugaban kamfanin SAGAMA HOMES da SAGAMA Construction & Engineering Ltd, Alhaji Ali Nuhu, ya ziyarci wani gidan marayu a jihar Kano, inda ya kai tallafin kayan abinci domin tallafa wa marayu da masu kula da su.
Tallafin ya ƙunshi shinkafa, taliya, man girki da sauran kayan abinci domin rage musu ɗimbin buƙatu, musamman a wannan lokaci na tsadar kayan masarufi.
Yayin ziyarar, Alhaji Ali Nuhu ya bayyana cewa wannan aiki wani ɓangare ne na ɗawainiyar SAGAMA wajen taimakon al’umma, tare da nuna kulawa ga mabukata.
> “Kula da marayu da marasa galihu nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa cikin al’umma. Wannan tallafi kaɗan ne idan aka kwatanta da ainihin abin da ake buƙata, amma mataki ne na tallafawa waɗannan yara,” in ji shi.
Shugabancin gidan marayun ya nuna matuƙar godiya bisa wannan ziyara da tallafin, tare da yi masa addu’ar samun nasara a rayuwarsa da ayyukansa.