Majalisar dokokin Kano ta amince da ƙarin Naira biliyan 215.3 a kasafin kudin jihar

0
12

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da ƙwarya-ƙwaryan kasafin kuɗi na naira biliyan 215.3 bayan tattaunawar da ƴan majalisar suka gudanar a zaman majalisa na yau Litinin.

Wannan amincewa ta biyo bayan buƙatar da Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya aika, inda Kakakin majalisar, Jibril Ismail Falgore, ya jagoranci zaman.

A wata sanarwa da mai magana da yawun Kakakin, Kamaluddeen Sani Shawai, ya fitar a ranar Litinin, an bayyana cewa jimillar kuɗin ƙarin kasafin ya kai ₦215,378,374,543.62.

Kakakin ya tabbatar da cewa ‘yan majalisa za su sa ido sosai wajen aiwatar da kasafin, tare da tabbatar da cewa kuɗaɗen da aka ware wa ma’aikatu da hukumomi za a yi amfani da su ta hanyar da ta dace.

Majalisar ta amince da kudirin bayan doguwar muhawara da kuma duba cikakken bayani daga mambobi kafin ƙarshe ta zartar da shi a matsayin doka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here