Ganduje na shirin samar da makoma ga wasu jami’an Hisbah da ake zargin sun rasa aikin su

0
20

Kwamitin da tsohon gwamnan Kano kuma shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya kafa domin binciken zargin korar jami’an Hisba da gwamnatin Kano ta yi, ya gudanar da zama na farko.

Shugaban kwamitin, wanda kuma shi ne Daraktan Hukumar Kula da  Nagarta Ayyuka ta Ƙasa, Baffa Babba Dan’Agundi, ya bayyana cewa aikin kwamitin shi ne tantance jami’an Hisba da ake zargin an kora daga aiki domin nemo musu makoma.

Kwamitin wanda ya ƙunshi mutum bakwai ya amince da kafa wakilci na mutum 44 daga kowacce karamar hukuma a jihar Kano.

Kwamitin dai na son samar da makoma ga waɗanda suka rasa ayyukan nasu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here