Cacar baki ta barke tsakanin El-Rufa’i da gwamnatin tarayya akan tsaro

0
8

Sabuwar muhawara mai zafi ta kunno kai tsakanin tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, da gwamnatin tarayya, bayan da ya zargi gwamnati da ƙarfafa ƴan bindiga ta hanyar ba su kuɗaɗe da abinci maimakon kawar da su.

El-Rufa’i ya yi wannan magana ne a hirarsa da Channels TV, inda ya ce tsarin gwamnatin na jawo matsalar tsaro ta ƙara ta’azzara. Ya bayyana cewa a maimakon hukunta masu laifi, ana yin  sulhu dasu da kuma biyan wasu alawus-alawus.

Sai dai ofishin mai bawa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya karyata wannan zargi, yana mai cewa “farfaganda ce marar tushe”. Ya ce a wannan gwamnati babu inda aka taɓa biyan kuɗin fansa ga ƴan bindiga, sannan jami’an tsaro sun samu nasarori masu yawa kamar kama shugabannin Ansaru da kashe manyan ƴan bindiga a Kaduna da wasu jihohi.

Ribadu ya ƙara da cewa gwamnati na amfani da dabaru biyu wajen yaƙi da matsalar tsaro, wato ƙarfin bindiga da kuma lalama, inda ya ce an samu sauƙi musamman a wasu yankunan Kaduna.

Sai dai al’ummar jihohi irin su Katsina, Zamfara da Kaduna na ci gaba da fuskantar hare-hare da asarar rayuka, lamarin da ke nuna cewa matsalar tsaro har yanzu na ci gaba da ƙalubale.

Masu nazari na ganin akwai rarrabuwar kai tsakanin masu goyon bayan amfani da ƙarfin soji kaɗai, da kuma waɗanda ke ganin akwai buƙatar tattaunawa da masu laifi don kawo ƙarshen rikicin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here