Ban damu da yadda mutanen Kudancin Kaduna ke ji a kaina ba–El-Rufa’i

0
16

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya ce ba ya damuwa da yadda abokan adawar sa musamman daga Kudancin Kaduna suke ji a kansa ba.

El-Rufa’i ya bayyana haka ne a cikin wata hira da ya yi da Channels Television a shirin Sunday Politics, inda ya ce mafi yawan mutanen da ke ganin shi mai tsattsauran ra’ayi ne, ba su taɓa sanin sa ko aiki da shi ba.

“Ban damu ba. Mutanen da suke ganin ni mai tsattsauran ra’ayi ne, ba su taɓa gani na ba, ba su san ni ba. Sun faɗi ra’ayinsu ne kawai. Gaskiya ne, dalilin da yasa makiya na ke tsananin ƙiyayya gare Ni, shi ne saboda ban damu da tunaninsu ba. Ni haka nake, kuma ina jin daɗin hakan,” in ji shi.

Da aka tambaye shi kan ra’ayin da wasu ke da shi cewa salon mulkin sa ya nuna wariya ga mutanen Kudancin Kaduna, El-Rufa’i ya karyata hakan.

“Su na iya tunanin abin da suka ga dama. Ni ban yarda da shirme ba; mulki ba wasa ba ne. A lokacin da nake mulkin mutane miliyan 10, dole ne a rika zama da kowa da adalci. Babu wanda zai iya zuwa ya ce saboda Kirista ne doka ba ta shafe shi ba. Akwai wasu daga Kudancin Kaduna da suke jin dole a bar su su yi abin da suka ga dama, amma ni ban yarda da haka ba,” in ji shi.

Ya kuma kara da cewa daga cikin mutanen da suka fi kusanci da shi a gwamnatin sa akwai ‘yan Kudancin Kaduna, don haka ba gaskiya ba ne cewa ya nuna musu wariya.

El-Rufa’i ya ce a lokacin mulkinsa ya dakatar da wasu dabi’u marasa kyau tare da rage yawan kashe kuɗin gwamnati a abubuwan banza.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here