Rikicin ’yan bindiga ya sake kazanta a Ƙaramar Hukumar Shagari ta Jihar Sakkwato, inda aka kashe akalla mutum biyar tare da yin garkuwa da limamai da hakimin garin Rinaye.
Shaidu daga yankin sun ce hare-haren sun ci gaba tsawon kwanaki uku a jere, inda ’yan bindigar ke kai farmaki kauyuka daban-daban, suna kashe mutane tare da sace wasu. A garin Rinaye, an tabbatar da cewa sun yi garkuwa da mai garin da limaman garin, bayan sun kashe mutum uku.
Rahotanni sun nuna cewa sama da kauyuka goma sun watse sakamakon tsanantawar hare-haren, lamarin da ya tilastawa daruruwan mazauna yankin yin zanga-zanga a babbar hanyar da ta haɗa Sokoto, Kebbi da Neja domin nuna fushi da rashin kulawar gwamnati gare su.
Wasu daga cikin mutanen da abin ya shafa sun ce ba su da wani tallafi daga gwamnati ko jami’an tsaro, inda suka yi kira da a kawo musu ɗauki cikin gaggawa.
Hukumomin bayar da agajin gaggawa na ƙasa dana jihar NEMA da SEMA sun tabbatar da samun rahoton ’yan gudun hijira daga yankin, inda suka ce sun kai ziyara wasu rukunin gidaje da suka karɓi waɗanda suka tsere daga hare-haren.