Rundunar ’yan sandan jihar Kaduna ta bayyana cewa ta kaddamar da bincike kan rikicin siyasa da ya barke a wani taron siyasa da aka ce tsohon gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufai, ya shirya.
Rahotanni sun nuna cewa a ranar Asabar wasu matasa dauke da makamai irin su adduna, kulake da duwatsu suka tarwatsa bikin kaddamar da kwamitin sauyi na jam’iyyar ADC a Kaduna. An ce sun jikkata mutane da dama tare da lalata motocin da ke wajen taron.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Mansir Hassan, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa taron an shirya shi ba tare da sanar da ’yan sanda da sauran jami’an tsaro ba duk da gargadin da aka rika yi.
A cewar shi, binciken farko ya nuna cewa rikicin ya samo asali ne daga arangama tsakanin magoya bayan mabanbantan ƴan siyasa, kuma an ce wasu daga cikin su sun yi amfani, lamarin da ya tayar da hankulan jama’a.
Hassan ya kara da cewa rundunar ta fara bincike a ofishin jam’iyyar ADC, inda shugabancin jam’iyyar ya musanta sanin wani taro, tare da bayyana goyon bayansu ga bin doka da oda.