Tsohon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Solomon Arase, Ya Rasu

0
7

Rahotanni sun tabbatar da rasuwar tsohon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (IGP) kuma tsohon Shugaban Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yan Sanda (PSC), Solomon Arase.

Arase ya riga mu gidan gaskiya a asibitin Cedarcrest da ke Abuja, duk da cewa har yanzu cikakken bayani game da rasuwar sa bai fito daga iyalansa ko kuma rundunar ‘yan sanda ba.

Shi ne shugaban ƴan sandan ƙasa na 18 a tarihin Najeriya, inda ya jagoranci rundunar daga Afrilu 2015 zuwa Yuni 2016 kafin ya yi ritaya. Daga bisani, tsohon shugaban kasa marigayi Muhammadu Buhari ya nada shi shugaban PSC a Janairu 2023, sai dai shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sauke shi daga mukamin a watan Yuni na 2024.

An haifi Arase a ranar 21 ga Yuni 1956 a karamar hukumar Owan West ta jihar Edo. Ya kammala karatunsa a fannin siyasa a jami’ar Ahmadu Bello, Zaria, sannan ya shiga rundunar ‘yan sanda a ranar 1 ga Disamba, 1981. Ya kuma yi karatun lauya a Jami’ar Benin, tare da samun digiri na biyu a Jami’ar Legas.

Kafin ya zama shugaban ƴan sandan ƙasa, Arase ya shugabanci sashen leken asiri na rundunar (CID), ya kuma rike mukamai daban-daban ciki har da Kwamishinan ‘yan sanda a jihar Akwa Ibom da AIG mai kula da leken asiri.

Ya kuma yi aiki a karkashin rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Namibia. Haka kuma, yana daga cikin manyan abokan hadin gwiwar makarantar sojin NDA.

Ya yi ritaya daga aiki a ranar 21 ga Yuni, 2016, bayan ya kai shekarun ritaya da doka ta tanada.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here