Trump ya kori ma’aikatan VOA sama da 500

0
6

Gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump, ta dauki matakin korar ma’aikatan gidan yada labarai na gwamnati, Voice of America (VOA), inda sama da mutum 500 suka samu takardar sallama daga aiki.

Shugabar rikon kwarya ta VOA, Kari Lake, ce ta bayyana hakan a shafinta na sada zumunta, tana mai cewa matakin zai baiwa sabuwar gwamnati damar tafiyar da al’amuran ta cikin sauki tare da rage nauyin haraji da ake kashe wa kafar.

Sai dai masana na ganin akwai yiwuwar wannan mataki zai fuskanci kalubale a kotu.

VOA dai an kafa ta ne a lokacin yakin duniya na biyu, domin yaƙi da farfagandar da gwamnatin Nazi ke yadawa a wancan lokaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here