Tinubu ya yiwa kowane yanki adalci a aikin raya ƙasa—Gwamnatin tarayya

0
13
Bola Tinubu
Bola Tinubu

Gwamnatin Tarayya ta ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana tafiyar da mulki bisa adalci da gaskiya wajen raba manyan ayyukan raya ƙasa da nade-naden gwamnati a dukkanin sassan Najeriya.

Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, wanda ya fitar da sanarwar hakan a Abuja, ya ce duk da jita-jitar da ake yadawa, babu wani yanki da aka yi watsi da shi.

 Ya ce ana gudanar da manyan ayyuka kamar hanyoyi, jiragen ƙasa, wutar lantarki da gyaran asibitoci a lokaci guda a fadin ƙasa.

Ya bayyana cewa bisa ga bayanan da suka tabbata, ga yadda aka raba kuɗaɗen ayyuka zuwa yankuna:

  • Arewa maso Yamma: Naira triliyan 5.97.
  • Kudu maso Kudu: Naira triliyan 2.41.
  • Arewa ta Tsakiya: Naira triliyan 1.13.
  • Kudu maso Gabas: Naira biliyan 407.
  • Arewa maso Gabas: Naira biliyan 400.
  • Kudu maso Yamma, Naira biliyan 604, amma banda, kuɗaɗen da aka kashe a Legas.

Ministan ya ce wannan rabon da kuma ci gaban ayyuka a fadin ƙasa ya nuna cewa Shugaba Tinubu yana mulki ne don gaba ɗaya Najeriya, ba wai don yankuna kaɗan ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here