Gwamnonin jihohin arewa maso gabas sun yi gargadi kan yiwuwar fuskantar karancin abinci a shekarar 2026 sakamakon tsadar kayan aikin gona da manoma ke fuskanta.
Wannan na ƙunshe ne a cikin sanarwar ƙarshen taro na 12 da Kungiyar Gwamnonin Arewa maso Gabas (NEGF) ta gudanar a Jalingo, jihar Taraba, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Babagana Umara Zulum na Borno, wanda shi ne shugaban kungiyar.
Gwamnonin sun ce dole ne a gaggauta ɗaukar matakai, musamman ta hanyar ƙara tallafin manoma da kuma inganta shirye-shiryen aikin gona na damina da na bazara domin kauce wa matsalar.
Dangane da wutar lantarki, gwamnonin sun ce za a ƙirƙiri shirin ci gaba na yankin, tare da mai da hankali kan amfani da hasken rana a matsayin hanya mafi sauƙi don samar da wuta ga al’ummomi.
Kungiyar NEGF ta ƙunshi gwamnonin jihohin Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe.