Gwamnatin Sokoto ta sanya limamai a tsarin albashin wata-wata

0
7

Gwamnatin Jihar Sokoto ta sanar da cewa za ta fara bayar da tallafin kuɗi na wata–wata ga masallatan Juma’a a faɗin jihar domin gudanar da ayyukan masallatai, tare da bai wa limamai, na’ibai da ladanai alawus na musamman.

Mai magana da yawun gwamnatin jihar, Abubakar Bawa, ya bayyana cewa wannan mataki na daga cikin shirye-shiryen gwamnati na bunƙasa karatun Alƙur’ani da kuma yaɗa ilimin addini a tsakanin matasa.

Gwamna Ahmed Aliyu ya tabbatar da hakan a wani biki na yaye daliban makarantar gidauniyar Sheikh Dahiru Bauchi da ke Sokoto, inda dalibai 111 suka kammala haddar Alƙur’ani.

Ya ce gwamnatin ta bayar da kwangilar gyaran masallatai 65 na Juma’a, inda aka kammala 25, sannan aka buɗe guda 15 cikin su. Haka kuma, an tanadi kuɗaɗe tsakanin Naira 300,000 zuwa 500,000 ga kowanne masallaci, tare da alawus ga limamai da sauran ma’aikatan masallatai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here