Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kafa kwamitin mutane 11 domin binciken zargin sayar da Kasuwar Yanka Dabbobi ta Chalawa, da aka gina tun 1980, wanda ake zargin ya faru a lokacin mulkin tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
Kwamitin, wanda Sakataren Gwamnatin Jiha, Alhaji Umar Faruq Ibrahim, ya kaddamar a ranar 27 ga Agusta, 2025, na karkashin jagorancin Barrister Muhuyi Magaji Rimin-Gado. An ba su umarnin tantance dukkan takardun shari’a da suka shafi cinikin, gano wadanda ke da hannu, bayar da shawarwari kan hukunci, da kuma bada tsari na sake kafa sabuwar kasuwar yanka dabbobi da
ta dace da zamani.
Kasuwar yanka dabbobi ta Chalawa ita ce mafi girma a Najeriya a lokacin da aka kammala ta a 1980 karkashin gwamnatin Muhammadu Abubakar Rimi, bayan da aka fara tunanin samar da ita a zamanin Audu Bako. An kashe sama da Naira miliyan 10 wajen gina ta kudin da a wancan lokaci aka ɗauka a matsayin mai yawan gaske. Ta ƙunshi kayan aikin sarrafa dabbobi daban-daban, rumbun ajiya na dubban dabbobi, da kuma tsarin gyaran kayayyakin da suka fito daga jikinsu.
Kwamitin na fuskantar babban aiki na dawo da martabar kasuwar yanka dabbobi, wacce aka yi amfani da ita wajen samar da abinci mai tsafta, ayyukan yi, da kuma inganta sunan Kano a fannin kasuwancin nama. Masana harkokin mulki suna ganin kafa wannan kwamiti a matsayin matakin jarumtaka da zai iya zama tubalin sake gina wata sabuwar kasuwar yanka dabbobi ta zamani ta hanyar haÉ—in gwiwar gwamnati da masu zuba jari.
Masu ruwa da tsaki sun bayyana cewa sake farfado da wannan waje na tarihi zai zama alamar gyara, da kuma hanyar dawo da amincewar jama’a ga gwamnati.