Wata mata mai suna Amaye, wadda ke sana’ar girki a garin Kasuwan-Garba na karamar hukumar Mariga, Jihar Neja, ta rasa ranta bayan da wasu mazauna yankin suka kai mata hari bisa zargin ta yi maganganu na batanci ga Annabi Muhammadu (SAW).
Rahotanni sun bayyana cewa an fara kai matar fadar Dagacin garin, inda daga bisani aka mika ta ga jami’an tsaro domin gudanar da bincike. Sai dai kafin a kai ga hakan, wasu fusatattun mutane sun mamaye jami’an tsaron tare da kashe matar, sannan suka banka mata wuta.
Shugaban karamar hukumar Mariga, Abbas Adamu Kasuwan-Garba, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce zuwa yanzu zaman lafiya ya dawo a yankin.
Haka zalika, kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na rana ranar Asabar, 30 ga Agusta, 2025. Ya ce tuni rundunar ta fara bincike tare da shirye-shiryen kama wadanda suka aikata wannan aika-aika domin gurfanar da su a gaban kuliya.