Tsohon Gwamnan jihar Jigawa kuma jigo a jam’iyyar PDP, Alhaji Sule Lamido, ya bayyana cewa ba zai dace ba ace wani ɗan Arewa mai tunani mai kyau ya sake zaɓar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben shugaban ƙasa na 2027 ba.
Lamido ya yi wannan magana ne a wani taron shugabannin PDP da aka gudanar a Dutse, babban birnin Jigawa.
Ya zargi gwamnatin APC da kawo wa ‘yan Najeriya wahala, yaudara da cin amana.
Tun farko mun gaya wa jama’a cewa Tinubu ba ya son Arewa, kuma ba ya son komai da zai taimaka wajen cigaban Arewa. A lokacin da yake gwamnan Legas, ‘yan Arewa sun sha wariya, an ci zarafinsu, har ma an kashe su,” in ji shi.
Lamido ya ce a 2023 manyan ƙungiyoyi kamar ACF, Ohanaeze da Afenifere ba su goyi bayan Tinubu ba, sai dai ya yi amfani da kudi wajen samun nasara.